Sunshine Online RadioNajeriya za ta zarta Amurka a yawan al’umma – MDD

Wani binciken Majalisar dinkin duniya ya yi hasashen cewa Najeriya za ta zama kasa ta uku a yawan al’uma a duniya kafin shekarar 2050.

Binciken ya nuna cewa Najeriya za ta zarta Amurka a yawan jama’a kafin shekarar ta 2050.

Haka kuma an yi hasashen cewa zuwa watan Nuwamban 2022 yawan al’umar duniya zai kai kusan biliyan takwas.

Binciken ya kuma nuna cewa yawan al’umar Indiya zai zarta na China a shakarar 2023

A yanzu dai yawan al’umar duniya ya kai biliyan 7.6, ana kuma hasashen zai kai biliyan 8.6 a 2030, sai biliyan 9.8 a shekarar 2050, sannan ya kai biliyan 11.2 a shekarar 2100.

@bbchausa

EU ta amince bai wa Ukraine da Moldova damar zama mambobinta

AFP – KENZO TRIBOUILLARD

Shugabannin Tarayyar Turai sun amince da bai wa Ukraine da Moldova da ke fama da yaki, takarar shiga Kungiyar EU a wani mataki na nuna goyon bayansu kan mamayar da Rasha ta yiwa kasar.

Shugaban EU Charles Michel yayin wani taron koli a Brussels, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa wani muhimmin mataki ne da aka baiwa kasashen na shiga Kungiyar.Tuni shugaban Ukraine din Volodymyr Zelensky ya jinjinawa shugabannin turai bisa wannan dama.Tabbatar da matsayin shiga takara shine matakin farko na shiga EU, tsarin da ke daukar shekaru kafin kasa ta zama mamba.

Rasha dai na gab da kwace manyan biranen Severodonetsk da Lysychansk da ke yankin gabashin Donbas na Ukraine, kuma karbar biranen biyu zai baiwa kasar ikon daukacin Lugansk, daya daga cikin yankuna biyu masu makwabtaka da Donetsk wanda ke da cibiyar masana’antar Ukraine ta Donbas.Yanzu haka dai Jamus na neman mafita game da batun iskar gas, bayan ta samu katsewar sa daga rashan, bayan da wasu kasashen Turai suka yanke alakar kasuwancin gas din da Rasha saboda kin biyan ta da kudin ruble.Yayin da shugaban Amurka Joe Biden zai gana da shugabannin Birtaniya, Canada, Faransa, Jamus, Italiya, da Japan a taron da za a yi a Bavaria kafin ya tafi Madrid don halartar taron NATO,Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi kira ga shugabannin kasashen Brazil, Indiya, China da Afirka ta Kudu da suka kasance abokan kawancen Rasha a kungiyar da ake kira BRICS da su ba ta hadin kai domin tunkarar takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata.

Daga rfi Hausa