Sunshine Online RadioShugaba Buhari zai tafi kasar Ghana

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi kasar Ghana ranar Asabar domin halartar taron kungiyar kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS.
Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai ranar Juma’a ta ce shugaban kasar zai bar Abuja a ranar ta Asabar domin haduwa da sauran shugabannin kasashen kungiyar ta ECOWAS, in ban da Mali wacce aka dakatar daga cikin kungiyar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi.
Ana sa ran tsohon shugaban Najeiya kuma manzo na musamman a kungiyar ECOWAS da ke sasanta rikicin kasar Mali Goodluck Jonathan zai gabatar da rahotonsa ga shugabannin kasashen kungiyar kan ziyarar da ya kai kasar Mali kwanakin baya.
Kazalika shugabannin kasashen kungiyar za su karbi rahoto kan sauye-sayen da za a yi a tsarin ECOWAS, ciki har da shirinta na samar da kudin bai-daya da kuma batun karba-karbar da kasashen kungiyar za su yi a takarar shugabancin kungiyar Kasashen Afirka wato African Union.
Wasu ministoci za su raka Shugaba Buhari a tafiyar da zai yi, cikinsu har da Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyema, da karamin Ministan ma’aikatar , Zubairu Dada, da Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), da Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, da Ministar Kudi da Tsare-Tsare da Kasafin Kudi, Zainab Ahmed.

@bbchausa

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *