
Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta ce an shafe makwanni 2 curr ba tare da annobar Korona ta halakawa kowa ba a kasar.
An shafe makwanni 2 ba tare Korona ta kashe kowa a Najeriya ba
Cikin sanawar da ta wallafa a shafinta na yanar gizo cibiyar ta ce samun nasarar ya sanya har yanzu adadin wadanda cutar Koronar ta kashe a Najeriya tsayawa a mutane dubu 2 da 117.
Sai dai tayi gargadin cewa ana cigaba da samun masu kamuwa da cutar, inda a ranar Juma’ar da ta gabata aka gano karin mutane 13.
Sabbin alkaluman da cibiyar dakile yaduwar cutukan ta NCDC ta fitar sun nuna an yiwa mutane miliyan 2 da dubu 231 da 409 gwajin cutar Korona a Najeriya, yayin da mutane dubu 163 da 540 suka warke daga cikin dubu 167 da 155 da suka kamu da cutar.