Sunshine Online RadioBorno Na Shirin Ba Manoma Damar Komawa Gonakinsu

A ranar Lahadi Zulum ya yi rangadin yankin hanyar ta Mulai zuwa Dalwa don ganewa idonsa yadda za a tsara bude hanyar.

Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ayyana shirinta na sake bude filayen gonaki da ke kan hanyar Molai zuwa Dalwa a jihar.

Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce, Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara yankin na Mulai da Dalwa, ya kuma gana da jami’an tsaro kan yadda za a shirya bude gonakin don manoma su fara yin aiki.

“Wannan mataki da Zulum ya dauka, ya biyo bayan umarnin da aka ba jami’an tsaron Najeriya a ranar Alhamis na ‘Operation Hadin Kai’ kan su hada kai da gwamanatin Borno, kan yadda za a ba mutane damar komawa gonakinsu.”

A ranar Lahadi Zulum ya yi rangadin yankin hanyar ta Mulai zuwa Dalwa.

Yayin ziyarar kwana daya da ya kai a makon da ya gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya ba dakarun kasar umarnin su hada kai da hukumomin da manoman jihar kan yadda za a sama masu hanyoyin da za su koma bakin aiki hade masu ayyukan kamun kifi.

Shi dai gwamna Zulum, ya sha nanata cewa, idan aka hana al’umomin da aka sauyawa matsuguni hanyar kai wa ga gonakinsu, akwai yiwuwar a fuskanci matsalar karancin abinci a jihar.

Ya kuma nanata cewa, tallafin abinci da ake samu daga kungiyoyin kasashen ketare da masu ba da gudunmowa na cikin gida, ba zai isa ba.

Manoma a jihar Borno, wacce ta dade tana fama da matsalar hare-haren Bokor Haram, sun kauracewa gonakinsu ala tilas saboda rashin tsaro.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *