
Cutar ta janyo wa tattalin arzikin duniya tafiyar hawainiya.
Rahoton da aka fitar ya ce an samu raguwar da dala triliyan ɗaya da biliyan 500 zuwa dala tiriliyan ɗaya ya nuna raguwar da aka dade ba a gani ba cikin shekara 16.
Har wa yau, zuba jari a kasashen duniya da na cikin gida su ma sun ragu, yayin da aka samu raguwar kudaden shiga da wanda ake batarwa ciki har da sayan motoci da gine-gine da sufuri da sauransu.
Hukumar ta MDD ta ce ana sa ran za a samu zuba jari a rubu’in karshe na shekarar nan, watakila a samu karuwar da kashi 15 cikin 100.
@bbchausa