Sunshine Online RadioAhmad Alhassan

EU ta amince bai wa Ukraine da Moldova damar zama mambobinta

AFP – KENZO TRIBOUILLARD

Shugabannin Tarayyar Turai sun amince da bai wa Ukraine da Moldova da ke fama da yaki, takarar shiga Kungiyar EU a wani mataki na nuna goyon bayansu kan mamayar da Rasha ta yiwa kasar.

Shugaban EU Charles Michel yayin wani taron koli a Brussels, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa wani muhimmin mataki ne da aka baiwa kasashen na shiga Kungiyar.Tuni shugaban Ukraine din Volodymyr Zelensky ya jinjinawa shugabannin turai bisa wannan dama.Tabbatar da matsayin shiga takara shine matakin farko na shiga EU, tsarin da ke daukar shekaru kafin kasa ta zama mamba.

Rasha dai na gab da kwace manyan biranen Severodonetsk da Lysychansk da ke yankin gabashin Donbas na Ukraine, kuma karbar biranen biyu zai baiwa kasar ikon daukacin Lugansk, daya daga cikin yankuna biyu masu makwabtaka da Donetsk wanda ke da cibiyar masana’antar Ukraine ta Donbas.Yanzu haka dai Jamus na neman mafita game da batun iskar gas, bayan ta samu katsewar sa daga rashan, bayan da wasu kasashen Turai suka yanke alakar kasuwancin gas din da Rasha saboda kin biyan ta da kudin ruble.Yayin da shugaban Amurka Joe Biden zai gana da shugabannin Birtaniya, Canada, Faransa, Jamus, Italiya, da Japan a taron da za a yi a Bavaria kafin ya tafi Madrid don halartar taron NATO,Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi kira ga shugabannin kasashen Brazil, Indiya, China da Afirka ta Kudu da suka kasance abokan kawancen Rasha a kungiyar da ake kira BRICS da su ba ta hadin kai domin tunkarar takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata.

Daga rfi Hausa

Shekau ne da kansa ya kashe kansa – Salkida

Encyclopedia

Kwararren mai bada bayanai akan Boko Haram Ahmad Salkida ya tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram.

Salkida ya bayyana a shafinsa na Twitter cewar anyi arangama tsakanin Shekau da kuma kungiyar ISWAP, Wanda suka bukaci ya mika wuya bori ya hau. Sai dai ba tare da wani bata lokaci ba Shekau din ha tashi nakiyar dake boye a rigan sa.

An dade ana samu takun saka tsakanin Boko Haram da ISWAP wanda har takan kai ga asarana rayuka a tsakaninsu.

Wasu jiragen kasa 2 sun yi karo da juna tare da hallaka mutane 32 a Masar.

Fiye da mutane 60 suka jikkata a hadarin jirgin mafi muni da Masar ta gani a shekarun baya-bayan nan.

Fiye da mutane 60 suka jikkata a hadarin jirgin mafi muni da Masar ta gani a shekarun baya-bayan nan. REUTERS – STRINGER

Akalla mutane 32 suka rasa rayukansu yayinda wasu 66 suka jikkata a wani hadarin jiragen kasa na fasinja guda biyu da suka yi taho mu gama da juna a kudancin kasar Masar yau Juma’a.

Hadarin wanda ke matsayin mafi muni da kasar ta gani a baya-bayan nan, ma’aikatar lafiyar kasar ta ce tuni aka aike da jerin motocin daukar marasa lafiya tare da jami’an agajin gaggawa don kai dauki yankin da lamarin ya faru.

Bayanai sun ce Jiragen sun ci karo ne a kudancin Masar, daya daga cikin jiragen yana hanyar shi ne ta zuwa Luxor da Alqahira yayinda dayan jirgin kuma ya ke hanyar shi ta tafiya Cairo da kuma kudancin birnin Aswan.

Tuni dai shugaba Abdel Fattah al Sisi ya sha alwashin hukunta duk wadanda ke da hanu a haddasa afkuwar hadarin.

Hukumar kula da jiragen kasa ta Masar ta ce, wasu fasinjojin da ba asan ko su wanene ba sun yi ta yunkurin tsayar da jirgin ta hanyar janyo waigi ko kuma igiyar tsayar da jirgin na gaggawa wanda ya haddasa matsala ga birkin jirgin da ya kai ga karkacewarsa daga layin dogo.

@ rfi Hausa

Covic19: masu tafiyar hawainiya na fuskantar barazanar kamuwa da covic19 ninki 4 – Bincike.

An buga binciken a cikin International Journal of Obesity

Mutanen da ke tafiya a hankali na fuskantar barazana ninki huɗu da kuma mutuwa daga Covid-19, wani sabon bincike ya gano.


Masu binciken kiwon lafiya da ke zaune a Leicester sunce masu tafiyar hawainiya da nauyi, sun fi yiwuwar mutuwa da cutar sau 3.75 fiye da masu saurin tafiya.
Aikin binciken ya yi amfani da bayanan da aka tattara daga fiye da mutane masu matsakaicin shekaru 400,000.


Jagoran mai binciken Farfesa Tom Yates ya ce za a iya amfani da saurin tafiya kai tsaye don yin hasashen ko wani na cikin hatsarin kamuwa da kwayar cuta. Nazarin, wanda Cibiyar Nazarin Kiwon Lafiya ta Kasa (NIHR) ta gudanar a Cibiyar Bincike na Kimiyyar dake Leicester, an tsara shi ne don gano alakar da ke tsakanin yawan ma’aunin jiki (BMI) da kuma saurin tafiya kai tsaye tare da hadarin kamuwa da mummunan Covid-19 da mace-mace.

Anyi amfani da rahoton kai da dai daga mutane 412,596 waɗanda ke shiga cikin, cibiyar nazarin halittu da bincike.

Tafiyar hawaniya yana nufin cimma tazaran kasa da mil uku ko kilomita(4.8) a kowace sa’a, yayin da ake bukatan tafiyan mil uku zuwa huɗu (6.4km) a kowace sa’a.

Masu binciken sun kuma gano cewa masu jan kafa wajen tafiya suna fuskantar barazana da yakai 2.5 daga tsananin Covid-19 fiye da wadanda ke cikin sashi mafi sauri.

Farfesa Yates, ƙwararren masani kan motsa jiki, na Jami’ar Leicester, ya ce: “Mun riga mun san cewa kiba da rashin ƙarfi sune manyan abubuwan haɗari ga sakamakon Covid-19. “Wannan shi ne bincike na farko da ya nuna cewa masu tafiyar hawainiya na da matukar hatsarin kamuwa da mummunan cutar Covid-19, ba tare da la’akari da nauyinsu ba.

Shugaban Tanzania John Magufuli ya mutu

Shugaban Tanzania Johon Magafuli, ya mutu yana da shekaru 61 a duniya bayan share tsawon kwanaki ana rade-raden cewa yana fama da rashin lafiya.

Mataimakiyar shugaban kasar Samia Suluhu Hassan wadda tabbatar da wannan labari, ta ce Magafuli ya mutu ne sakamakon fama da ciwon zuwa.

Samia ta ce ranar 17 ga watan Maris na shekarar 2021 da misalin karshe 6 na yamma, shugaba John Pombe Joseph Magafuli ya rasu a asibitin Mzena da ke birnin Dares Salaam.

Tsohon shugaban kasar Tanzania, marigayi John Magufuli.
Tsohon shugaban kasar Tanzania, marigayi John Magufuli. AP – Stringer

Da farko dai an kwantar da shugaban ne ranar 6 ga watan Maris a asibitin Jakaya Kikwete don ba shi kulawa sakamakon rashin lafiyar ta ciwon zuciya da yake fama da shi kimanin shekaru 10.PUBLICITÉ

Tuni aka fara shirye-shiryen jana’izar marigayin, tare da ware kwanaki 14 domin zaman makoki a duk fadin kasar, bayan sauko da tutar kasar zuwa kasa.

Daga cikin abubuwan da za a rika tuna marigayi John Magufuli shugaban Tanzania na 5, akwai aiki tukuru da yayi wajen samawa al’ummarsa kayayyakin more rayuwa abinda ya sa ake kiransa da sunan ‘Bulldozer’ wato Sarkin aiki.

Marigayi John Magufuli.
Marigayi John Magufuli. AP – Khalfan Said

Marigayi Magufuli ya kuma raba albashinsa gida 4 inda yake daukar kashi 1.

Batu na baya bayan nan kuma da za a rika tuna tsohon shugaban na Tanzania da shi, shi ne yin watsi da wanzuwar annobar Korona, bayan da ya ce binciken sirrin da ya sanya aka yi, ya gano cewar Akuya, man fetur da kuma gwanda sun kamu da cutar, dan haka akwai lauje cikin nadi dangane da barkewar annobar.

@ Rfi Hausa