Sunshine Online RadioBai wa tsaffin hafsoshin tsaro mukamin jakadu tukuici ne ga sadaukarwarsu – fadar shugaban kasa

Fadar shugaban Najeriya ta bayyana zaben tsaffin manyan hafsoshin tsaron kasar da gwamnati ta sallama a matsayin jakadun kasar da cewa tukuici ne na aiki da sadaukarwa da suka yi.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya sanya wa hannu a yau Lahadi.

Garba Shehu ya kuma caccaki babbar jam’iyyar adawa ta kasar PDP a game da kiran da ta yi na gurfanar da hafsoshin sojin gaban kotu.

A ranar Alhamis ne shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da sunayen su Gabriel Olonisakin, tsohon hafsan hafsoshin kasa; Tukur Buratai, tsohon babban hafsan soji; Abubakar Sadique, tsohon babban hafsan sojin sama da Ibok Ibas, tsohon babban hafsan sojin ruwa ga majalisar dattawar kasar domin tantancewa.

Wannan mataki na shugaban Najeriya na zuwa ne kimaninn mako guda bayan murabus din su.

 

 

Shugaban Kungiyar Tarayar Afrika Moussa Faki Ya Sami Zarcewa Wa’adi Na Biyu

Tsohon Firaministan Chadi Moussa Faki Mahamat ya sami zarcewa wa’adi na biyu na tsawon shekaru hudu na shugabancin kungiyar Tarayar Afrika.

Shugabannin kasashen kungiyar suka amince da wannan zarcewa a taron su ta bidiyo na kwanaki biyu da suka fara Asabar.

Faki wanda ya kasance babu hamayya a takaran ta sa ya sami kuri’u 51 daga cikin wakilai 55 a zaben da aka yi cikin sirri.

Taron na shugabannin kasashen Africa ta bidiyo na zuwa ne shekara daya bayan da kasar Masar ta sami mutun na farko da ya harbu da kwayar cutar Coronavirus, al’amarinda ya haifar da fargaba a kasashen nahiyar.

Taron na kwanaki biyu ta bidiyo na duba matsalar cutar Coronavirus a nahiyar da sauran matsalolin rashin tsaro.

Coronavirus ta haddasa gagarumin koma baya a yaki da Cancer- WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi kan yadda yaki da cutar Coronavirus ke shirin haddasa nakasu a kokarin da ake na bayar da kulawa ga masu fama da cutar Cancer a sassan Duniya.

Shugaban hukumar WHO shiyyar Turai Hans Kluge a jawabinsa kan ranar kula da masu ciwon Cancer ta Duniya, ya ce duk daya cikin kasashen Turai 3 yanzu na fuskantar babban tashin hankali wajen kula da masu cutar ta Cancer.

A cewar jami’in, hankulan kasashen Duniya ya karkata kacokan wajen yaki da Coronavirus wanda ya tilasta kasashe 53 da ke cikin WHO da kaso mai yawa a tsakiyar Asiya da kuma Turai fuskantar babban kalubale wajen kula da masu Cancer sakamakon yadda ko dai sashen da aka warewa cutar ya fuskanci nakasu ko kuma ya durkushe baki daya.

Sanarwar da Kluge ya fitar yau Alhamis ya ce kasashe da dama ciki har da masu matukar arziki sun fuskanci karancin magunguna kula da masu cutar ta Cancer yayinda wasu kuma suka kawar da kai daga sashen kula da masu Cancer dungurugum tare da bayar da fifiko ga yaki da Coronavirus.

A kasashen Netherlands da Belgium yayin kullen da kasashe suka gani a 2020 masu fama da Cancer sun fuskanci karancin kulawa daga kashi 40 zuwa 30 yayinda tsarin kula da Cancer a Kyrgyzstan ya ragu zuwa kashi 90, batun Mr Hans Kluge ke bayyanawa da babban abin damuwa a yaki da cutar ta Cancer a Duniya.

Haka zalika Mr Kluge ya bayyana damuwa kan yadda hasashe ke nuna yiwuwar samun karuwar mace mace sanadiyyar Cancer a Birtaniya kadai da kashi 15 yayinda za a samu karuwar masu fama da Cancer mama da kashi 9 nan da shekaru 5 masu zuwa.

Buhari ya nada Burutai da Sadiq Jakadun Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da sunayen tsoffin manyan hafsoshin sojin da ya sauke ga Majalisar Dattawa domin amincewa da su a matsayin Jakadun Najeriya.

A wasikar da shugaba Buhari ya gabatarwa Majalisar, ya bayyana sunan Janar Abayomi Olanisakin da Janar Tukur Yusuf Buratai da Admiral Ibok-Eté da Marshal Sadiq Abubakar da kuma Marshal Mohammed Usman a matsayin Jakadu.

Sanarwar da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya rabawa manema labarai tace, Buhari ya bukaci Majalisar da ta gaggauta amincewa da sunayen domin tura su inda zasu gudanar da ayyukan su.